Hilda Baci, za ta dafa buhun shinkafa 250 a gasar tukunyar jollof mafi girma ta duniya
Daga Jameel Lawan Yakasai
Mai rike da lambar yabo ta duniya ta Guinness, Hilda Baci, ta bayyana cewa za ta yi amfani da buhunan shinkafa 250 a yunkurinta na dafa abin da zai zama tukunyar jollof mafi girma a duniya.
Baci, wadda ta kafa tarihin tseren dafa abinci mafi dadewa a duniya a shekarar 2023, ta yi cikakkun bayanai a cikin wani faifan bidiyo da aka saka a Instagram ranar Litinin, yayin da take nazarin girman aikin.
KU KUMA KARANTA: ‘Yar Najeriyar na yunƙurin lashe gasar girki ta Guinness
Ta bayyana cewa, katuwar tukunyar da za a yi wa wannan katafariyar gasa tana da karfin lita 22,619, inda ta kara da cewa burinta shi ne ta cika ta zuwa kashi 80 cikin dari.









