Hauhawar farashi a Najeriya ta ƙaru zuwa kashi 34.19 a watan Yuni

0
87
Hauhawar farashi a Najeriya ta ƙaru zuwa kashi 34.19 a watan Yuni

Hauhawar farashi a Najeriya ta ƙaru zuwa kashi 34.19 a watan Yuni

Hukumar ƙididdiga ta Najeriya (NBS) ta bayyana cewa an samu ƙaruwar hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar a watan Yuni zuwa kashi 34.19 a yayin da ‘yan ƙasar ke ci gaba da fama da tsadar rayuwa.

NBS ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na intanet ranar Litinin.

Hakan na nufin an samu ƙaruwar hauhawar farashi da kashi 0.24 idan aka kwatanta da alƙaluman watan Mayun 2024 da hukumar ta fitar.

“A watan Yunin 2024, an samu ƙaruwar hauhawar farashi zuwa kashi 34.19 idan aka kwatanta da watan Mayun 2024 inda hauhawar farashin ta kai kashi 33.95. Idan aka aka kwatanta alƙaluman, za a ga cewa an samu ƙaruwar hauhawar farashi da kashi 0.24,” in ji NBS.

Hukumar ƙididdiga ta Najeriya ta ƙara da cewa alƙaluman farashi na shekara-shekara sun nuna cewa hauhawar farashi ta ƙaru da kashi 11.40 idan aka kwatanta da a watan Yunin shekarar 2023.

KU KUMA KARANTA: Za mu raba wa jami’an tsaro tallafin abinci — Gwamnan Kano

NBS ta fitar da alƙaluman ne kwanaki kaɗan bayan Shugaba Bola Tinubu ya yi umarni a shigo da kayan abinci Najeriya tare da cire haraji daga kansu na tsawon kwana 150 da zummar rage hauhawar farashinsu a ƙasar.

Wasu dai sun yaba wa wannan mataki yayin da wasu ke cewa matakin zai rage karsashin manoman Najeriya waɗanda suka daɗe suna roƙon gwamnati ta sauƙaka musu hanyoyin noma domin noma abincin da za su ciyar da ƙasar.

Leave a Reply