A yammacin ranar Laraba ne wani mummunan hatsari ya afku a jihar Sokoto wanda ya rutsa da ayarin mataimakin gwamna Idris Gobir, wanda yayi sanadin asarar rayuka biyu.
Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa yace, wata motar ‘yan sanda da ke cikin ayarin motocin ɗauke da jami’an yan sanda da mai ɗaukar hoto Buhari Tanko ta yi hatsarin.
Majiyar ta tabbatar da cewa jami’an ‘yan sandan da ba a tantance ko su waye ba da kuma mai ɗaukar hoto Tanko sun rasa rayukansu a wurin.
Da yake bayyana alhinin lamarin, majiyar ta ce, “Na tabbatar da cewa motar da ta yi hatsarin motar ‘yan sanda ce, inda mai ɗaukar hoton na tare da su a cikin mota lokacin da lamarin ya faru. Abin takaici ne kuma abin baƙin ciki ne.”
KU KUMA KARANTA: Mutum 11 sun mutu a hatsarin mota a Jigawa
A halin da ake ciki, Gwamna Ahmed Sokoto, tare da mataimakin gwamnan, ya jagoranci wata tawaga zuwa Sabon Birni domin gudanar da ayyuka.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Ahmed Rufa’i, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da wata mota a cikin ayarin mataimakin gwamnan.
Kuma an tabbatar da mutuwar direban motar, jami’in ‘yan sanda, tare da mutum ɗaya, mai ɗaukar hoto a cikin ayarin.
Mutanen da suka samu raunuka a hatsarin na ci gaba da karɓar magani a asibitin koyarwa na Jami’ar Usman Ɗanfodiyo da ke Sakkwato.