Aƙalla mutum 11 ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin wata tirela da ya auku a hanyar Maiyama/Koko da ke Jihar Kebbi.
Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kebbi, Nafiu Abubakar ya fitar, ya ce motar na ɗauke da fasinjoji 65, waɗanda dukkaninsu maza ne daga Jihar Sakkwato.
Bayan fasinjojin, tirelar na kuma ɗauke da buhun albasa da buhun wake da babura shida da ta taso daga ƙaramar hukumar Goronyo da ke Sakkwato zuwa Jihar Neja.
“A lokacin da direban motar ya kai kusa da ƙauyen Dada, a ƙaramar hukumar Koko/Besse, birki ya kwace wa direban motar.
“Saboda haka, babbar motar ita kaɗai ta shiga daji. Sakamakon haka, fasinjoji 65, dukkaninsu maza daga Jihar Sakkwato, ciki har da direban sun samu munanan raunuka.”
KU KUMA KARANTA: Motar ƴan sanda ta yi hatsari a Kebbi
Da samun rahoton faruwar hatsarin, Abubakar ya ce an aike da tawagar ‘yan sandan da ke kula da zirga-zirgar ababen hawa daga sashin Koko zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka kai waɗanda lamarin ya rutsa da su babban asibitin Koko.
Ya ce yayin da aka tabbatar da mutuwar mutum 11, sauran waɗanda abin ya shafa ana duba lafiyarsu a asibitin.
Da yake mayar da martani kan lamarin, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Chris Omonzokpea Aimionowane, ya yi addu’ar Allah Ya jikan waɗanda suka rasu.
Ya kuma yi wa waɗanda suka jikkata fatan samun lafiya, tare da gargaɗin direbobi da su guji wuce gona da iri da kuma tuƙin ganganci.