No menu items!

Sample Page Title

Date:

Hatsarin tirela a Ibadan ya murƙushe mutane 25

Wani hatsarin mota ya laƙume rayukan ’yan arewa 18 da wasu mutane 7, a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.

Hatsarin da ya laƙume rayuka 25 a ranar Talata, ya auku ne a daidai mararrabar Agbowo Ajao a kan babbar hanyar Oyo zuwa Iwo.

Wani da lamarin ya auku a kan idanunsa ya ce burki ne ya ƙwace daga direban wata tirela da ke ɗauke da banduran kwanukan rufi inda a nan take ya danne wasu ƙananan motoci uku masu ɗauke da fasinjoji a cikinsu.

Sarkin Hausawan Ojo Tudun-Sunnah da lamarin ya auku a kusa da fadarsa, ya shaida wa Aminiya cewa “a binciken da muka gudanar mun gano cewa ɗaya daga cikin motocin da haɗarin ya rutsa da su wata motar bas ce mai ɗaukar mutane 18 da ta taso daga Jihar Jigawa a kan hanyar zuwa Legas.”

KU KUMA KARANTA: Hatsarin jirgin ruwa ya laƙume rayukan mutane 9 a Zamfara

Sarkin Hausawan ya ce duka fasinjoji 18 da ke cikin wannan motar bas sun gamu da ajalinsu.

Ya ce, “yanzu haka al’ummar Hausawa a nan Ojo Tudun-Sunnah sun taimaka da kudin sayen likkafani domin suturta waɗannan ’yan uwa Musulmi da za a yi masu jana’iza da binne su a makabartar Akinyele inda aka saba binne musulmi ’yan Arewa da suka riga mu gidan gaskiya.”

Sauran mutanen da ke cikin ƙananan motocin da tirelar ta murƙushe an kwashe gawarsu zuwa Asibiti.

Har zuwa lokacin rubuta wannan rahoto babu wani bayani a hukumance da aka samu dangane da wannan hatsari.

Sai dai binciken ya nuna cewa kafin isowar jami’an tsaro an ga jama’a suna kai ɗauki domin ceton waɗanda suka samu raunuka a wajen hatsarin.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...