Aƙalla mutum 12 ne ajali ya katsewa hanzari ciki har da yara biyu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su a ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.
Lamarin, kamar yadda wani ganau ya shaida wa wakilinmu, ya ce ya faru ne da misalin ƙarfe 1:20 na rana a kan babbar hanyar Funtuwa zuwa Tsafe.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, hatsarin ya rutsa da mutum 24 — 22 a cikin wata motar haya da wasu mutum biyu a wata A-Kori-Kura ƙirar Toyota.
Hatsarin wanda ya auku a sakamakon tsautsayi, bayanai sun ce an yi taho-mu-gama ne tsakanin motocin yayin da gudanarwar motar hayar ta ƙwace daga hannun direbanta.
Yanzu haka dai an kwantar da waɗanda suka jikkata a Babban Asibitin Tsafe, inda suke karɓar magani.
KU KUMA KARANTA: Mutane bakwai sun mutu, 40 sun jikkata a wani hatsarin mota a Yobe
Wani jami’in Hukumar Kiyaye Haɗurra ta ƙasa (FRSC) da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya alaƙanta aukuwar hatsarin da tuƙin ganganci.
“Ina cikin jami’an FRSC da suka kai ɗauki wurin da hatsarin ya faru wanda ya rusta da mutum 24 a duk motocin biyu.
“Waɗanda suka mutu sun haɗa wasu mutum 10 da ƙananan yara biyu, yayin da kuma da dama suka jikkata,” a cewarsa.