Hatsarin mota ya kashe mutane 5 ‘yan gida ɗaya a Kano
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Mazauna garin Ɗambatta da ke Kano sun shiga cikin firgici, sakamakon rashin da sukayi na rasuwar mutane Biyar.
Hadarin dai ya faru kilometer bakwai kafin shiga garin Dambatta lokacin da mutanen ke dawowa daga jihar Bauchi bayan sun raka amarya.
KU KUMA KARANTA:Hatsarin mota ya ci rayukan mutane 5 a Yobe
Daga cikin waɗanda suka rasu akwai yayan wani mutum mai suna Alhaji Surajo guda biyu da kuma yayan kaninsa Alhaji Salisu Dan Raino guda uku.
Tuni aka yi Jana’izarsu kamar yadda addinin musulunci ya tana da









