Hatsarin mota ya ci rayukan mutane biyar a hanyar Legas zuwa Ibadan

1
181

Mutane biyar ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya auku a gaban sansanin Foursquare, dake kan titin Legas zuwa Ibadan a safiyar ranar Lahadi.

Lamarin, a cikin wata sanarwa da hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC), sashin ilimin jama’a, reshen jihar Ogun, Florence Okpe, ta fitar, ya faru ne da misalin ƙarfe 6:15 na safe.

An bayyana cewa, jimillar mutane 21, waɗanda dukkansu manya maza ne suka yi hatsarin, inda mutane 12 suka samu raunuka, biyar kuma ba a samu raunuka ba.

Motoci guda uku, wata babbar motar DAF mai lamba KMC 810ZB; Toyota Bus mai lamba TMA 244 XA da wata motar bas Mitsubishi wacce babu lambar rajista a ciki.

Okpe ya ce, abubuwan da ake zargin sun haddasa haɗarin ne sakamakon wuce gona da iri; Taya ta fashe tare da rasa iko daga ɓangaren direban motar wanda hakan ya sa wasu motocin suka kutsa cikinta.

KU KUMA KARANTA: Wani ɗan sanda a Anambra ya mutu a hatsarin mota

Kwamandan sashen na FRSC Anthony Uga, ya shawarci masu ababen hawa da su guji amfani da tayoyin da ba su dace ba, sannan su riƙa amfani da ƙa’idojin saurin hankali musamman a wannan lokacin damina.

1 COMMENT

Leave a Reply