No menu items!

Sample Page Title

Date:

Aƙalla mutane 14 ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a ƙauyen Zangoro dake kan hanyar Bauchi zuwa Darazo.

Kwamandan sashin na hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa FRSC a jihar Bauchi Yusuf Abdullahi ne ya bayyana hakan a wani hatsarin mota da ya auku a ranar Alhamis a Bauchi.

Ya ce wasu mutane biyar sun samu mummunan raunuka daban-daban a haɗarin wanda ya faru a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 12:17 na rana.

KU KUMA KARANTA: Hatsarin mota ya ci rayukan ‘yan sanda uku a Kaduna

A cewarsa, hatsarin ya haɗa da mota ƙirar Golf 3 Wagon mai lamba AJ507GWA da wata mota ƙirar Chevrolet mai zaman kanta.

Kwamandan ya alaƙanta hatsarin da sauri da gudun wuce ƙa’ida, inda ya ƙara da cewa jami’an hukumar sun wanke wurin da hatsarin ya auku tare da ƙwato Naira dubu 73,000, wayoyi bakwai, ‘power bank’ ɗaya da ƙananan jakunkuna huɗu.

“Mutane 19 ne suka mutu a hatsarin motar, wanda suka haɗa da manyan mata 10, manyan maza bakwai, yara mace ɗaya da namiji ɗaya. “Goma sha huɗu daga cikinsu sun rasa rayukansu a nan take sun haɗa da manyan mata 10, manyan maza biyu, yaro namiji ɗaya da mace ɗaya,” inji shi.

Abdullahi ya ce an miƙa gawarwakin waɗanda suka mutu da waɗanda suka jikkata zuwa asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi domin kula da lafiyarsu da kuma tantance su.

Ya shawarci masu ababen hawa da su mutunta ƙa’idojin zirga-zirgar ababen hawa a lokacin da suke tafiyar da hanya.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

4 COMMENTS

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...