Hatsabibin ɗan daba da ake nema ruwa a jallo a Kano, ya miƙa kansa tare da mabiyansa 40

Wani ɗan daba mai suna “Abba Burakita” da aka bayyana ana nema ruwa a jallo ya miƙa kansa ga rundunar ‘yan sandan jihar Kano tare da mabiyansa guda 40.

Idan ba a manta ba a baya kwamishinan ‘yan sandan jihar CP ya bayyana cewa ana neman Abba da wasu manyan ‘yan daba guda biyu tare da yin alƙawarin bayar da tukuicin Naira dubu 100 ga duk wanda ya bayar da bayanan da suka kai ga kama su.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba, 2023, ya ce Abba Barakita bisa son ransa ya miƙa kansa ga ‘yan sanda tare da sanar da tuba daga ayyukan ‘yan daba.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *