Harin da Isra’ila ta kai a Gaza ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama

0
30
Harin da Isra'ila ta kai a Gaza ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama

Harin da Isra’ila ta kai a Gaza ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama

Aƙalla Falasɗinawa 15 da suka haɗa da ƙananan yara ne suka mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata, a wani harin da Isra’ila ta kai kan wani matsuguni da ke Khan Younis a kudancin Gaza a yammacin Lahadi, a cewar wata majiyar kiwon lafiya.

Shaidu sun ba da rahoton cewa, an kai harin ne a makarantar Ahmed Abdel Aziz, inda ɗaruruwan fararen hula da suka rasa matsugunansu suka nemi mafaƙa.

KU KUMA KARANTA: Farmaƙin Isaraila ta sama ya kashe aƙalla mutane 18 a Gaza.

Hukumar tsaron kiyaye farar hula ta Gaza ta tabbatar da harin, inda ta ce tawagogin likitocin sun gano gawarwaki da dama. Sai dai har yanzu ba a fayyace adadin yaran da abin ya shafa ba.

Leave a Reply