Har yanzu ina fatan mijina zai dawo gida – matar Dadiyata

Khadija Ahmed Lame, uwargidan fitaccen sanannen ɗan dandalin sada zumuntan nan Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata, ta bayyana fatanta na cewa maigidanta zai dawo gida wata rana.

Tun a ranar 2 ga watan Agustan shekarar 2019 ne Dadiyata ya ɓace, yayin da wasu da ba a san ko su waye ba suka haɗa shi cikin motar sa suka tafi da shi.

Malamin mai shekaru 34, an ce yana cikin gidansa da ke Barnawa, Kaduna, a lokacin da maharan suka kai harin.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun yi barazanar auran matan da aka sace a Zamfara, sun buƙaci a ba su naira miliyan 12 (Bidiyo)

Da take magana da Sashen Hausa na BBC a ranar Laraba, Misis Lame ta ce tunkarar ɓacewar mijinta shekaru huɗu da suka wuce ya yi mata tsauri da ‘ya’yanta.

“Ba zan iya kwatanta yadda nake ji ba, amma abin baƙin ciki ne. Ban taɓa tunanin zai ɗauki tsawon wannan lokaci bai dawo ba.

A gaskiya ban taɓa tunanin ya ɓace kwana ɗaya ba, ga shi nan muna ƙirga shekaru huɗu.Yana da ban tsoro kwarai da gaske, ”in ji ta.

Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf, ya yi alƙawarin gudanar da bincike kan ɓacewar Dadiyata.

Sai dai Misis Lame ta ce har yanzu ba a tuntuɓi dangin ba kan wani bincike da aka gudanar.

“Da farko an so mu yarda cewa ana gudanar da bincike, amma har yanzu babu wani abu da ya fito daga ciki.

“Kuma babu wanda ma yake magana da mu, sai dai alƙawarin da gwamnan Kano ya ɗauka kwanan nan.

Kuma ban ma sani ba ko sun fara binciken kamar yadda suka yi alƙawari saboda babu wanda ya tuntuɓe mu,” inji ta.

Misis Lame ta kuma bayyana cewa tana yi wa ‘ya’yanta biyu ƙarya cewa mahaifinsu ya yi tafiya kuma zai dawo nan ba da daɗewa ba.

Tambayoyi suka riƙa yi, kuma ina roƙonsu da su yi haƙuri kuma zai dawo nan ba da daɗewa ba,” in ji ta.

Dangane da yadda dangin suka kasance cikin shekarun da suka gabata, ta ce abokai da dangin mijinta da ya ɓace suna tallafa wa dangin.

Da aka tambaye ta ko har yanzu tana da begen sake saduwa da mijinta, mahaifiyar ’ya’ya biyu ta ce: “Na yi imani zai dawo.

Ban taɓa tunanin cewa ya tafi har abada ba. Za mu sake haɗuwa, da yardar Allah.

Don haka ina da ƙwarin gwiwa cewa zai dawo”. “Ina ƙira ga sabuwar gwamnati da duk wanda ke da ikon ceto mijina da ya yi haka, don Allah.

Ina tsoron ka da duk ƙaryar da nake yi wa ’ya’yana za ta tonu nan ba da jimawa ba.

“Kowace rana mai albarka, ina roƙonsu da ka da su damu mahaifinsu zai dawo. Kuma har yanzu bai dawo ba.

Ba na son yaran su gan ni a matsayin maƙaryaciya,” in ji ta.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *