Har yanzu farashin man fetur bai kai matakin da ya kamata ya kai ba a Najeriya — IMF

0
97
Har yanzu farashin man fetur bai kai matakin da ya kamata ya kai ba a Najeriya — IMF

Har yanzu farashin man fetur bai kai matakin da ya kamata ya kai ba a Najeriya — IMF

Asusun Lamuni na Duniya (IMF), ya ce har yanzu ba a kai farashin man fetur ɗin asalin farashinsa na kasuwa ba a Najeriya.

Hakan na nuni da cewa za a iya ƙara farashin a nan gaba kamar yadda jaridar Vanguard ta rawaito ta bakin Babban wakilin IMF a Najeriya, Dokta Christian Ebeke a yayi da yake jawabi a tattaunawarsa da gidan talabijin na Arise TV a jiya Alhamis.

Sai dai kuma adaidai lokacin da ake ci gaba da muhawara a kan ƙarin farashin man fetur, Asusun Lamuni na Duniya, IMF, ya buƙaci gwamnatin Najeriya da ta ba ɓangaren rage wa talakawan ƙasar raɗaɗi muhimmanci.

Babban jami’in na IMF ya bayyana damuwarsa a kan irin wahalar da ƴan Najeriya suke ciki a sanadiyar wasu matakai da gwamnatin ƙasar ta ɗauka.

KU KUMA KARANTA:Ba mu yarda da ƙarin farashin man fetur ba – Marasa rinjaye a majalisar wakilai

A cewar Ebeke, “Ina tunanin ƙarin farashin man ya zo ne a daidai lokacin da ƴan Najeriya suke cikin tsananin rayuwa.

“Ƴan Najeriya suna fama da matsaloli da dama kamar hauhawar farashin kayayyaki kamar su abinci ga ambaliya da sauransu.

“Don haka ƙara farashin man sai ya zo a daidai lokacin da tattalin arzikin ƙasar ke tangal-tangal, kuma ƴan Najeriya ke cikin tsananin rayuwa.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here