Har yanzu ba mu samu labarin fitar Nijar, Mali da Burkina Faso daga cikinmu ba – ECOWAS

0
164

Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta ce har yanzu a hukumance ƙasashen Mali, Burkina Faso da Nijar ba su sanar da ita matakinsu na fita daga cikinta ba.

A ranar Lahadi da hantsi ƙasashen uku suka fitar da sanarwa cewa sun fice daga ƙungiyar saboda ta gaza taimaka musu wurin shawo kan rashin tsaron da ke addabasu da ma sauran ƙalubalen da suke fama da su.

“Har yanzu Hukumar ECOWAS ba ta samu bayani a hukumance daga ƙasashen uku ba da ke nuna cewa sun fita daga cikinta,” a cewar wata sanarwa da ECOWAS ta wallafa a shafinta na X.

Kungiyar ta ce ta yi mamakin “wannan mataki.”

ECOWAS ta ƙara da cewa tana “aiki babu kakkautawa da waɗannan ƙasashe domin ganin an dawo da tsarin mulki.”

KU KUMA KARANTA: Jamhuriyar Nijar, Burkina Faso da Mali sun fice daga ECOWAS

“Burkina Faso, Nijar, da Mali mambobinmu ne masu matuƙar muhimmanci kuma hukumar nan za ta yi baƙin ƙoƙarinta wurin samar da mafita ga rikicin siyasar da suke ciki.”

Leave a Reply