‘Yan sandan Isra’ila sun yi gargaɗin cewa sanya takunkumin hana shiga Masallacin Ƙudus a cikin watan Ramadan na iya ƙara ruruta wutar rikici a Birnin Ƙudus, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na ƙasar suka ruwaito.
Kwanan nan ne Minista mai tsattsauran ra’ayi Itamar Ben-Gvir ya yi kira da a daina barin mazauna Yammacin Kogin Jordan da Yahudawa suka mamaye su shiga wuri na uku mafi tsarki na Musulunci a lokacin azumin watan azumi, yayin da aka ba da izinin shiga ga Falasdinawa ‘yan Isra’ila masu shekaru 70 zuwa sama kawai.
Tashar talabijin ta Channel 12 ta Isra’ila ta rawaito wasu manyan jami’an ‘yan sanda da ba a bayyana sunayensu ba suna cewa za a yanke shawara kan lamarin a ƙarshen mako mai zuwa.
Jami’an sun ce idan aka yanke shawarar mayar da martani ga bukatun Ben-Gvir, hakan na iya ƙara ruruta wutar rikici a Birnin Ƙudus da aka mamaye, da kuma gauraye garuruwan da Isra’ila da Falasdinawa ke zaune.
KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta sanar da shirin ƙayyade adadin masu zuwa sallar Juma’a a Masallacin Al Aqsa
Ƙungiyar Abraham Initiatives ta aike da wasiƙa zuwa ga kwamishinan ‘yan sandan Isra’ila Yaakov Shabtai tana gargaɗin yiwuwar ta’azzarar rikicin.