No menu items!

Sample Page Title

Date:

Rundunar sojin ƙungiyar Hamas ta Falasɗinu ta bayyana cewa kawo ƙarshen hare-haren da Isra’ila ke kai wa Gaza shi suka fi fifitawa, tare da jaddada yin watsi da duk wata yarjejeniyar musaya ko tattaunawa inda har ba a cika wannan sharaɗi ba.

An bayyana hakan ne a cikin wani jawabin da Abu Ubaida, mai magana da yawun rundunar Al Qassam Brigades ya yi, wanda aka watsa a tashar talabijin ta Aljazeera.

Abu Ubaida ya sanar da cewa mayaƙan Al Qassam “sun lalata motocin soji fiye da 825, da suka haɗa da manyan motocin yaƙi da tankokin yaƙi tun farkon mamayar da Isra’ila ta kai ta ƙasa.”

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta kama wata babbar ‘yar siyasar Falasɗinu

Ya ƙara da cewa: “Abin da muka sa a gaba shi ne mu dakatar da kai hare-hare kan al’ummarmu a Gaza, kuma babu wani fifiko da ya wuce haka.”

Ya jaddada cewa “ba za mu amince da duk wata yarjejeniyar musaya ko shawarwari ba kafin a daina kai hare-hare kan al’ummarmu a Gaza.”

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...