Tsohon shugaban Gabon Bongo, an ba shi ‘yancin fita ƙasar waje

0
368

Tsohon shugaban ƙasar Gabon, Ali Bongo, wanda aka hamɓarar da shi, ya faɗa cikin tsaka mai wuya, yanzu yana da ‘yancin barin ƙasar ya tafi ƙasar waje, jagoran juyin mulkin da ya hamɓarar da shi yace a ranar Laraba.

“Yana da ‘yancin yin tafiya kuma yana iya tafiya ƙasashen waje idan ya ga dama,” in ji Janar Brice Oligui Nguema a wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na ƙasar.

Bongo, wanda ya shafe shekaru 14 a kan karagar mulki, ya kasance a gidan kaso tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 30 ga watan Agusta, ba tare da zubar da jini ba, ƙasa da sa’a guda bayan da jam’iyyarsa ta sanar da sake tsayawa takara a zaɓen da aka bayyana a matsayin maguɗi na masu ra’ayin riƙau.

KU KUMA KARANTA: Ƙasar Gabon ta sake buɗe iyakokin ƙasar – Sojoji

“Idan aka yi la’akari da yanayin lafiyarsa, tsohon shugaban ƙasar Ali Bongo Ondimba yana da ‘yancin yin tafiya.

Yana iya tafiya ƙasashen waje idan yana son gudanar da duba lafiyarsa,” in ji Kanar Ulrich Manfoumbi Manfoumbi, yayin da yake karanta wata sanarwa da Oligui ya sanyawa hannu ya rantse a matsayin shugaban riƙon ƙwarya a ranar Litinin.

Bongo ya yi fama da matsananciyar shanyewar jiki a watan Oktoban 2018 wanda hakan ya sa ya samu naƙasu a jiki, tare da wahala musamman wajen motsa ƙafarsa da hannu ta dama.

Leave a Reply