Gwarzon namijin da ya yi faɗa da Zaki na tsawon awa ɗaya don kare iyalinsa

0
239
Gwarzon namijin da ya yi faɗa da Zaki na tsawon awa ɗaya don kare iyalinsa

Gwarzon namijin da ya yi faɗa da Zaki na tsawon awa ɗaya don kare iyalinsa

Wani jarumi daga ƙasar Uganda ya gamu da mummunan rauni bayan ya yi mummunar fafatawa da wani Zaki tsawon fiye da awa ɗaya, domin kare iyalinsa daga hatsarin wannan ƙaƙƙarfan Zakin.

Wani abin mamaki kuma shi ne, babu makami a hannunsa, sai ya dogara da ƙarfin jikinsa da ƙarfin zuciya, inda ya nuna jarumta ta gaske wajen gwabzawa da dabba mai haɗari kamar Zaki har ya samu nasarar kashe shi.

KU KUMA KARANTA:Kotu a Indiya na son a sauya wa wani zaki da matarsa suna saboda taƙaddamar addini

Wannan lamari ya girgiza mutane da dama, kuma ya zama abin mamaki da ban al’ajabi, domin kowa ya san irin ƙarfi da haɗarin da ke tattare da Zakin daji.

Wannan jarumin ya nuna cewa soyayya da sadaukarwa ga iyali na iya sa mutum ya aikata abin da ba a za ta. A gaskiya, wannan abu ne da ya kamata a yaba da kuma karrama shi a kai.

Leave a Reply