Gwamnoni sun nemi a basu wata 3 kafin bawa ƙananan hukumomi kuɗinsu

0
40
Gwamnoni sun nemi a basu wata 3 kafin bawa ƙananan hukumomi kuɗinsu

Gwamnoni sun nemi a basu wata 3 kafin bawa ƙananan hukumomi kuɗinsu

Daga Ali Sanni Larabawa

Gwamnatin tarayyar da gwamnonin jihohin Najeriya sun cimma matsaya a kan bawa jihohi wa’adin wata uku kafin su tsame hannnunsu daga lamurran ƙananan hukumomi.

Hakan dai ya biyo bayan damuwar da jihohin suka nuna game da bawa ƙananan hukumomin ‘yancinsu nan-take saboda tasirin da hakan zai yi kan albashi da kuma wasu abubuwa da suke tarraya a kai.

Wannan dai na nufin ya zama dole ƙananan hukumomin su jira har nan da watan Oktoba kafin su fara samun kuɗaɗensu kai tsaye.

Gwamnan jihar Gombe Inuwa Yahaya, ya shaida wa manema labarai cewa, daga cikin abubuwan da aka tattauna yanzu an bawa jihohin da basu yi zaɓen ƙananan hukumomi ba damar su yi zaɓe, sannan wannan doka ta fara aiki, domin idan aka ce a fara ba wa ƙananan hukumomi kuɗaɗensu to inda ba’a yi zaɓe ba wa za’a bawa kenan?

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Najeriya ta fara tattaunawa da ‘yan kasuwa don karya farashin kayan abinci 

Bayan bawa jihohi damar gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi, zasu kuma kawo tsare-tsarensu domin akwai abubuwa da akwai haɗaka a ciki a tsakanin jihohi da kuma ƙananan hukumomi kamar ɓangaren ilimi wato hukumar SUBEB, da ɓangaren lafiya a matakin farko to shiyasa aka bada dama saboda kada a samu matsala.

Gwamna Yahaya, ya ƙara da cewa suna fatan zuwa watan Oktoban jihohin da basu yi zaɓe ba sunyi, sai doka ta fara aiki.

Masu sharhi kan lamuran yau da kullum na ganin ba wa ƙananan hukumomi ‘yancin cin gashin kai ne kawai zai iya kawo ƙarshen matsalar Najeriya saboda sune mafi kusa da jama’a kuma su suka fi sanin matsalolinsu ta yadda zasu magance su.

Sai dai wasu na ganin su ma suna da nasu laifukan wadanda ke da alaka da zargin cin hanci da rashawa, ko da yake sun sha musantawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here