Gwamnatin Yobe ta buƙaci jaridar PUNCH ta nemi afuwar al’umma kan yaɗa labaran ƙarya na kashe-kashe a jihar

0
258
Gwamnatin Yobe ta buƙaci jaridar PUNCH ta nemi afuwar al'umma kan yaɗa labaran ƙarya na kashe-kashe a jihar

Gwamnatin Yobe ta buƙaci jaridar PUNCH ta nemi afuwar al’umma kan yaɗa labaran ƙarya na kashe-kashe a jihar

Gwamnatin jihar Yobe ta yi kakkausar suka ga wani rahoto da jaridar Punch ta buga na zargin kisan gillar da aka yi a ƙauyen Mafa da ke ƙaramar hukumar Tarmuwa, inda ta bayyana shi a matsayin ƙarya, mara tushe, kuma yaudara.

A wata sanarwa da babban daraktan yaɗa labarai na Gwamna Mai Mala Buni, Mamman Mohammed ya fitar, Gwamnatin jihar Yobe ta buƙaci jaridar PUNCH ta gaggauta janye rahoton tare da neman afuwar jama’a a jihar Yobe musamman al’ummar Mafa.

Rahoton da ya jawo cece-ku-ce, wanda wani wai Ahmed Kagana Amshi, ya yi iƙirarin cewa an kashe mutane da dama tare da binne su a yankin. Sai dai hukumomi a jihar sun yi watsi da zargin da cewa ƙarya ce kawai tsagwaronta.

Sanarwar ta ce “A iya sanina, ƙauyen Mafa da jihar Yobe gaba ɗaya sun kasance cikin kwanciyar hankali, inda mazauna yankin ke gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali.”

KU KUMA KARANTA: Kwamishinan yaɗa labaran Yobe, Bego ya yaba wa Gwamna Buni kan nuna goyon baya ga ‘yan jarida (hotuna)

Ya ƙara da cewa rundunar ‘yansandan jihar Yobe, da ofishin mai ba da shawara na musamman kan harkokin tsaro, da shugaban ƙaramar hukumar Tarmuwa duk sun musanta faruwar lamarin.

Sanarwar ta bayyana jaridar PUNCH a matsayin “babban illa ga aikin jarida,” sanarwar ta soki jaridar Punch da yadda ta ba da damar buga irin wannan rahoto marar tushe, inda ta yi gargaɗin cewa sahihancin labaran da jaridar ke buga wa a yanzu ya zama a bar tambaya a idon jama’a.

Gwamnati ta buƙaci jama’a da su yi watsi da rahotannin jaridar gaba ɗayanta, tare da jaddada cewa ba ta da wani abu na gaskiya a cik.

Sanarwar ta ƙara da cewa “Wannan rahoton da ba gaskiya ba ne ya haifar da rauni na tunani da ba dole ba ga mutanen Mafa masu son zaman lafiya.”

Leave a Reply