Gwamnatin Yobe na shirin amincewa da bada tallafin rage raɗaɗi na naira dubu 35 ga ma’aikatan jihar

0
127

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

Gwamnatin Jihar Yobe na shirin amincewa da bada tallafin  kimanin  naira dubu N35,000 ga ma’aikatan gwamnatin Jihar don rage raɗaɗin wahalhalun da cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi ke haifarwa ga rayuwar ma’aikatan da iyalen su.

Sakataren Gwamnatin jihar ya kasance shugaban kwamitin da gwamna Mai Mala ya naɗa don duba lamarin.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun muƙaddashin shugaban ma’aikatan jihar, Hamidu M. Alhaji, kuma aka mikawa sakataren gwamnatin jiha, Baba Malam Wali a jiya Juma’a a garin Damaturu.

Tun farko ne dai Gwamna Mai Mala Buni ya amince da naɗin sakataren Gwamnatin jihar Alhaji Bana Malam Wali a matsayin shugaban wannan  kwamitin kan bayar da tallafin naira dubu N35,000 ga ma’aikatan gwamnatin.

KU KUMA KARANTA: Gwamna Buni ya ba da tallafin karatu ga ɗaliban koyon Shari’a kimanin 221 a Yobe

Sannan ya kuma bayyana cewa kwamitin na da mambobi shida tare da Babban Sakataren kula da ɓangaren ma’aikata a matsayin sakataren kwamitin.

Kwamitin zai tantance abin da ya shafi kuɗi na aiwatar da tallafin ga ma’aikatan da kuma yin shawarwari da ƙungiyoyin ƙwadago kan kuɗaɗen da za a amince da su a matsayin tallafin daga ɓangaren gwamnatin da kuma ƙungiyar ‘yan kwadago (NLC).

Leave a Reply