Gwamnatin Tinubu ba ta da alƙibila – Atiku
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce yanayin Gwamantin Tinubu daidai yake da mota a tsakiyar jeji babu direba.
Atiku ya bayyana gwamtin a matsayin mara alƙibila ce a yayin da yake sukan sabon tsarin da ta ɓullo da shi na haramta wa ɗalibai ‘yan ƙasa da shekaru 18 zana jarabawar kammala sakandare.
Dokar, “ta fito fili da ɗabi’ar Gwamnatin Tinubu, wadda take daidai da matuƙin jirin ruwan da ya ɓace a tsakiyar teku,” in ji shi.
A martanin da ya wallafa ranar Laraba a shafinsa na X, Atiku ya ce dokar ba komai ba ce face kassara harkar neman ilimi.
KU KUMA KARANTA: Sakacin gwamnati ne da jami’an tsaro kan kisan Sarkin Gobir – Atiku
Ana iya tuna cewa Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, ya riga ya sanar da cewa babu gudu babu ja da baya kan maganar shekaru 18 a matsayin mafi ƙarancin shekaru ga ɗalibai masu zana jarabawar shiga manyan makarantu.
Amma tsohon ɗan takararn shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023 din ya bayyana dokar a matsayin koma-baya ga harkar ilimi, domin kuwa dokar tane neman hana yancin neman ilimi.
A don haka ya ce ya kamata kowa ya fito ya yi tir da ita, inda ya ci gaba da cewa, “Tsarin mulkin Najeriya ya sanya ilimi a jerin ayyukan yau da kullum wadda gwamnatocin jihohi ke da ƙarfin iko a kai fiye da ta Tarayya.
“Saboda haka dokar ilimi da Gwamnatin Tarayya ta yi daidai yake da mulkin kama-karya.
“Abin da aka sani a ƙasashe shi ne jihohi su yi irin waɗannan dokoki a ɓangaren ilimi; abin haushin shi ne yadda gwamnatin ba ta yi wani tanadi domin ɗalibai masu basira ba, wanda hakan ke nuna ba ta san muhimmancinsu ba.“