Gwamnatin Tarayya zata haɗa hannu da Gwamnatin Jihar Kano domin gina cibiyar kasuwanci ta zamani
Daga Jameel Lawan Yakasai
Karamin Ministan Gidaje da Raya Birane, Rt. Hon. Yusuf Abdullahi Ata, ne ya bayyana hakan a yayin tarbar mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam, a ofishinsa da ke Abuja ranar Laraba.
Mai magana da yawun Mataimakin Gwamnan Ibrahim Shuaibu ya bayyanawa manema labarai cewa, Ziyarar ta mayar da hankali ne kan batun gina cibiyar masana’antu a Kano.
Gwamnatin jihar Kano ta yi alkawarin samar da filayen da suka dace domin saukaka ci gaban masana’antu, matakin da zai bunkasa ci gaban tattalin arzikin jihar da samar da sabbin damammaki ga mazauna jihar.
READ ALSO: An buɗe babbar kasuwar Singa a Kano bayan kammala aikin tsaftace magudanar ruwa
Wannan aiki dai ya yi daidai da kudirin gwamnatin tarayya na bunkasa masana’antu da habaka tattalin arziki a fadin kasar nan.
A yayin taron, Minista Ata da Mataimakin Gwamnan sun yi nazari kan hanyoyin hada hannu kan ayyukan gina gidaje da raya birane a jihar Kano.
Sannan sun bayyana kwarin guiwar wannan aiki zai kawo sauyi ga tattalin arzikin Jihar Kano da inganta rayuwa inda suka amince da ci gaba da karfafa dangantakar aiki don tabbatar da nasarar aiwatar da cibiyar masana’antu da sauran ayyukan hadin gwiwa.









