Gwamnatin tarayya zata biya Julius Berger biliyan 280 don kammalan titin Abuja zuwa Kano

0
102

Gwamnatin tarayya zata biya Julius Berger biliyan 280 don kammalan titin Abuja zuwa Kano

Daga Ali Sanni

Gwamnatin tarayya ta amince da biyan kanfanin aiki na Julius Berger naira biliyan ashirin a kowane wata har na tsawon watanni goma sha huɗu.

Ministan Ayyuka, David Umahi, ya bayyana cewa a duk wata za a biya kamfanin Naira biliyan 20 har na tsawon watanni 14 domin kamfanin ya kammala aikin kilomita 82 na ɓangaren da ya rage a aikin titin.

KU KUMA KARANTA:Yin titin da ya haɗa Dawasa, Kukuri da Chukuriwa zai bunƙasa harkokin kasuwanci a yankin – Mazauna yankin 

Ministan ya sanar da biyan wannan Naira biliyan 280 ne a yayin da yake kokawa kan ƙarancin kuɗaɗen gudanar da ayyukan hanyoyin.

Ya bayyana haka ne a wani zama da ya yi da Julius Berger kan ayyukan kwangilar manyan tituna da kamfanin yake gudanarwa, waɗanda Gwamnatin Tinubu ta gada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here