Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa

0
81
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa

Gwamnatin Tarayya ta yi alƙawarin tallafa wa jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa da Naira biliyan uku domin rage musu raɗaɗin halin da suke ciki.

Ministan Kuɗi da Harkokin Tattalin Arziƙi, Mista Wale Edun ne, ya sanar da haka yayin wata ziyara da ya kai Jihar Kebbi.

Ya bayyana cewa kuɗin zai taimaka wa jihohi kamar Kebbi su taimaka wa manomansu don noman damina mai zuwa, wanda yake da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da wadatar abinci da kuma rage hauhawar farashin kayayyaki.

KU KUMA KARANTA: Mutum 129 sun mutu, sama da 120 suka jikkata sakamakon ambaliyar ruwa

Edun, ya kuma bayyana aniyar Shugaba Bola Tinubu na taimaka wa waɗannan jihohi don ci gaba da samar da tsaro da kuma haɓaka samar da abinci.

Ministan Kasafi da Tsare-Tsare, Sanata Atiku Bagudu, ya nuna damuwa game da ɓarnar da ambaliyar ta yi, amma ya yaba da ƙoƙarin mutanen Jihar Kebbi.

Ya tabbatar da cewa gwamnati za ta tallafa musu don inganta noman damina.

Bugu da ƙari, Gwamnatin Tarayya ta amince da biyan kuɗi don aiwatar da ayyuka kamar hanyar Badagry zuwa Sakkwato da kuma faɗaɗa tsarin ban ruwa a kusa da hanyar, wadda za ta amfani Jihar Kebbi.

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya roƙi ƙarin tallafin Gwamnatin Tarayya, inda ya nuna damuwa kan lalacewar gonakin shinkafa.

Gwamna Idris ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta riga ta samar da kayayyaki ga manoma don taimaka musu game da noman damina.

Amma ya jaddada buƙatar taimakon Gwamnatin Tarayya saboda ƙalubalen da ambaliyar ruwa ta haifar a daminar bana.

Leave a Reply