Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da tallafin Naira miliyan 10 ga ma’aikatan makarantun gaba da sakandare
Daga Shafaatu Dauda Kano
Gwamnatin Tarayya a ranar Lahadi, ta bayyana sabon shirin tallafi na musamman ga ma’aikatan jami’o’i, kwalejojin ilimi da kuma manyan makarantu a fadin Najeriya, mai suna Tertiary Institution Staff Support Fund (TISSF). Wannan sanarwar ta fito ne daga bakin Daraktar Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Mrs Folasade Boriowo, a Abuja.
Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa ne ya kaddamar da shirin, inda ya bayyana shi a matsayin tsarin tallafi da zai inganta walwala da ci gaban ma’aikatan ilimi, ciki har da malaman dake koyar da darussa da kuma ma’aikatan da ba na koyarwa ba. Ya ce wannan yunkuri wani bangare ne na kokarin gwamnati na tallafa wa ma’aikata domin inganta harkar ilimi a matakin gaba da sakandare.
A cewar Ministan, kowane ma’aikaci da ya cancanta na da damar karbar lamuni har zuwa Naira miliyan goma (N10m), muddin bashin bai wuce kaso 33.3 cikin 100 na jimillar albashin sa na shekara guda ba. Daga cikin abubuwan da za a iya amfani da bashin a kai sun hada da siyan ababen hawa, kula da lafiya, da kuma zuba jari a kananan sana’o’i kamar kiwon kaji.
KU KUMA KARANTA: Gwamnatin tarayya ta sake buɗe shafin yanar gizo na ɗaukar sabbin ma’aikata a hukumomin tsaro
Za a gudanar da wannan shiri ne tare da hadin gwiwar Bankin Masana’antu (Bank of Industry), domin tabbatar da gaskiya da tsantseni wajen rabon kudaden. Wannan mataki yana daga cikin hanyoyin da gwamnati ke bi domin tabbatar da cewa kudin tallafin ya isa hannun masu bukata yadda ya kamata.
Dr. Alausa ya bayyana cewa wannan shiri na TISSF ya na da nasaba da burin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na sauya fasalin harkar ilimi a Najeriya. Ya ce: “Ba tallafi kawai ba ne; wannan wani tsarin karfafa gwiwa ne ga ma’aikatan ilimi domin su rayu cikin walwala, su samu cigaban sana’a, tare da bayar da gudunmuwa mai amfani ga makarantun da suke aiki.”









