No menu items!

Sample Page Title

Date:

Gwamnatin tarayya ta sanar da lokacin kammala aikin titin jirgin ƙasa daga Kaduna zuwa Kano

Daga Jameel Lawan Yakasai

Gwamnatin Najeriya ta ce za a kammala aikin titin jirgin ƙasa daga Kaduna zuwa Kano a cikin shekarar 2026 mai zuwa, kamar yadda Ministan Sufuri Sa’idu Ahmed Alkali ya bayyana.

Da yake magana yayin wani taron tuntuɓa tsakanin ‘yan ƙasa da gwamnati da ke gudana a jihar Kaduna da ke arewacin ƙasar, ministan ya ce lokacin da Shugaba Tinubu ya hau mulki kashi 15 cikin 10 na aikin kawai aka kammala.

“Amma zuwa yanzu an kammala kashi 53 cikin 100,” in ji shi cikin wata sanarwa da ma’aikatar yaɗa labarai ta fitar a yau Laraba.

KU KUMA KARANTA: Za a kammala aikin titin jirgin ƙasa na Abuja a watan Mayun 2024 – Sakataren Sufuri

A 2024 gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ta samu rancen kuɗin da za ta kammala aikin daga wani bankin kasuwanci na ƙasar China, abin da ministan ya jaddada a yau din.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...