Gwamnatin tarayya ta sake buɗe shafin yanar gizo na ɗaukar sabbin ma’aikata a hukumomin tsaro

0
256
Gwamnatin tarayya ta sake buɗe shafin yanar gizo na ɗaukar sabbin ma’aikata a hukumomin tsaro

Gwamnatin tarayya ta sake buɗe shafin yanar gizo na ɗaukar sabbin ma’aikata a hukumomin tsaro

Daga Jameel Lawan Yakasai

Hukumar gudanarwa ya hukumomin Civil Defence, hukumar kula da gidajen gyaran hali da hukumar kula da shige da fice wato(CDCFIB) ta sanar da sake buɗe shafin yanar gizo na ɗaukar sabbin ma’aikata, bayan dakatarwar da aka samu na ɗan lokaci saboda matsalolin yanar gizo.

Hukumar ta dakatar da aikin ɗaukar ma’aikata a hukumomi huɗu na tsaro da take kula da su, bayan da aka samu manyan matsaloli a shafin yanar gizon. A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin, CDCFIB ta tabbatar da cewa an gyara matsalolin kuma shafin ya koma aiki yadda ya kamata tare da ba da hakuri ga masu neman aikin kan tsaikon da suka fuskanta.

KU KUMA KARANTA: Tinubu ya ba da umarnin ɗaukar ma’aikatan lafiya 774 aiki

“Mun yi matuƙar ba da hakuri kan katsewar da aka samu a lokacin shigar da bayanan neman aiki. Saboda yawan masu neman aiki, dole ne mu inganta tsarin don tabbatar da cewa zai iya ɗaukar dukkan masu nema, domin samun tsarin ɗaukar ma’aikata mai sauƙi, gaskiya da adalci,” in ji sanarwar.

“Ku ziyarci adireshin shafinmu daga ranar 21 ga Yuli, 2025: https://recruitment.cdcfib.gov.ng,” in ji hukumar.

Leave a Reply