Gwamnatin Tarayya ta kwaso ‘yan Najeriya 190 gida daga Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa

0
46
Gwamnatin Tarayya ta kwaso ‘yan Najeriya 190 gida daga Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa

Gwamnatin Tarayya ta kwaso ‘yan Najeriya 190 gida daga Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa

Gwamnatin Tarayya ta kwaso ‘yan Najeriya 190 da suka maƙale a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa zuwa gida.

A cewar sanarwar da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), ta fitar mai ɗauke da sa hannun babban daraktanta mai kula da shiyar arewa ta tsakiya, Bashir Garga, a yau Talata, ta ce ayarin jami’an gwamnati ƙarƙashin jagorancin NEMA sun tarbi mutanen da suka dawo gidan a filin saukar jiragen saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja da misalin ƙarfe 5 da mintuna 57 na asuba.

NEMA ta ƙara da cewar hukumomin daya kamata sun dauki bayanan mutanen, tare da jan hankalinsu akan “zama mutane na gari” bayan da suka dawo Najeriya.

KU KUMA KARANTA: Shugaban Somalia ya yi tur da mummunan hari kan sojojin Daular Larabawa a Mogadishu

“Gwamnatin tarayya ta buƙaci ‘yan Najeriya, su zamo jakadun ƙasar nan na gari, tare da haɓɓaka aƙidun kishin ƙasa da bin doka da oda da zama sahihan mutane masu mutunci.”

Idan za’a tuna, a watan Oktoban 2022, gwamnatin tarayya ta dawo da jimillar mutane 542 gida daga Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here