Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin tabbatar da bai wa ƙananan hukumomin ‘yancinsu

0
72
Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin tabbatar da bai wa ƙananan hukumomin 'yancinsu

Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin tabbatar da bai wa ƙananan hukumomin ‘yancinsu

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta kafa wani kwamiti mai mutum goma da zai tabbatar da bin hukuncin Kotun Ƙoli na bai wa ƙananan hukumomi cin gashin kansu.

A ranar Talata ne Sakataren Gwamnatin Tarayya Sanata George Akume ya ƙaddamar da kwamitin mai ƙunshe da ɓangarori 10 don tabbatar da cewa an bi hukuncin da Kotun Ƙoli ta aiwatar a ranar 11 ga watan Yulin 2024 da ya ce a dinga bai wa ƙananan hukumomin Nijeriya kuɗaɗensu kai-tsaye.

Sanarwar da Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ya fitar ta ce: “Babban aikin kwamitin shi ne tabbatar da cewa an bai wa ƙananan hukumomi cikakken ‘yancin cin gashin kansu, da ba su damar yin aiki sosai ba tare da katsalandan ɗin gwamnatocin jihohi ba.

“Wannan matakin dai ya yi daidai da kokarin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu na ganin an aiwatar da tsarin da ya dace ga tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulki, wanda ya amince da kananan hukumomi a matsayin mataki na uku na gwamnati,” in ji sanarwar.

KU KUMA KARANTA: INEC ta fitar da farashin tsayawa takara na zaɓen ƙananan hukumomi a Kano

Mambobin kwamitin sun haɗa da:

Sakataren Gwamnatin Tarayya a matsayin Shugaban Kwamiti

Ministan Kuɗi da na Tattalin Arziki – Mamba

Atoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a – Mamba

Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki

Babban Akanta na Gwamnatin Tarayya
Gwamnan Babban Bankin Najeriya

Babban Sakataren Ma’aikatar Kuɗi

Shugaban Hukumar Tarawa da Kason Kuɗaɗen Shiga ta Ƙasa

Wakilan Gwamnnoni

Wakilan Ƙananan Hukumomi

A ranar 11 ga watan Yuli ne alkalin Kotun Koli Mai Shari’a Emmanuel Agimya umarci gwamnatin tarayya ta riƙa tura wa ƙananan hukumomin ƙasar 774 kuɗaɗensu kai-tsaye domin su riƙa gudanar da harkokinsu.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ce ta shigar da ƙara inda ta roƙi Kotun Ƙolin ta bari a riƙa tura wa ƙananan hukumomin kuɗaɗensu ba tare da katsalandan ɗin gwamnoni ba.

Kazalika alƙalin ya ce naɗin da gwamnoni suke yi wa shugabannin ƙananan hukumomi na riƙo ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya, yana mai cewa alhakinsu ne su gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi.

Tuni dai har wasu jihohin sun fara shirya zaɓukan ƙananan hukumomi a faɗin ƙasar har ma an gudanar da na wasu jihohin.

Leave a Reply