Gwamnatin tarayya ta gargaɗi Peter Obi akan yunƙurin kawo cikas ga zaman lafiyar ƙasa

1
307

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta gargaɗi ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Mista Peter Obi da ya guji tunzura jama’a zuwa ga tashin hankali kan sakamakon zaɓen shugaban ƙasa.

Ministan yaɗa labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya ba da wannan sanarwar a birnin Washington DC a lokacin da yake ganawa da wasu kungiyoyin yaɗa labarai na duniya.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, Ministan ya je Washington din ne domin tattauna wa da kungiyoyin yaɗa labarai na ƙasa da ƙasa da kuma cibiyar bincike ta ‘Think-tanks’ kan zaɓen 2023 da aka kammala a Nijeriya.

KU KUMA KARANTA: Magoya bayan jam’iyar LP na yunƙurin mamaye ofisoshin hukumar zaɓe

NAN ta kuma ruwaito cewa, kawo yanzu Ministan ya yi hulda da “Washington Post”, Muryar Amurka, Associated Press, da Mujallar Manufofin Kasashen Waje.

A lokacin tattaunawa daban-daban da kungiyoyin yada labarai, ministan ya ce, ba daidai ba ne Obi a wani fanni ya nemi a yi masa hukunci a kotu kan sakamakon zaɓen da kuma yadda yake kokarin ya sa mutane su ta da zaune tsaye.

“Obi da mataimakinsa, Datti Ahmed ba za su iya yi wa ‘yan Nijeriya barazana cewa idan aka rantsar da zaɓaɓɓen shugaban kasa, Bola Tinubu na jam’iyyar APC a ranar 29 ga watan Mayu, zai kawo karshen mulkin dimokuradiyya a Najeriya.

“Wannan cin amana ne. Ba za ku iya zama kuna gayyatar tayar da hankali ba, kuma abin da suke yi ke nan. “Maganar Obi na mutum ne mai yanke kauna, ba shi ne dan dimokradiyya da ya yi ikirarin zama ba.

“Bai kamata ɗan dimokradiyya ya yi imani da dimokuradiyya ba kawai idan ya ci zaɓe,” in ji shi.

Ministan ya ce, a kalubalantar sakamakon zaben, babu wata hanyar samun nasara ga Obi ko Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP.

A cewar ministan, Obi da Atiku sun gaza cika sharuddan da kundin tsarin mulkin kasar ya tanada na ayyana wa a matsayin shugaban kasa. “Tsarin mulki yana da tsayayyen sharuɗɗa ga duk wanda ke son zama shugaban ƙasar. “Ba wai kawai ya samu yawan ƙuri’un da aka kada a zabe ba, amma kuma ya samu kashi daya bisa huɗu na kuri’un da aka kada a akalla jihohi 25.

“Zabaɓɓen shugaban ƙasa ne kawai ya cika sharuɗɗan da ya samu ƙuri’u miliyan 8.79 da kuma kashi daya bisa hudu na kuri’un da aka kada a jihohi 29 na tarayya,” in ji shi.

Ministan ya ce Atiku wanda ya zo na biyu da kuri’u miliyan 6.9 ya samu kashi daya bisa hudu ne kawai na kuri’un da aka kada a jihohi 21. Ya ce Obi ya zo na uku da kuri’u miliyan 5.8 amma ya samu kashi daya bisa huɗu na ƙuri’un da aka kaɗa a jihohi 15.

“Ba za ku iya cin zaɓe a rumfunan zaɓe inda kuka zo matsayi na uku ba kuma kuka kasa cika ka’idojin tsarin mulki. “Peter Obi, yayin da yake korafin zamba bai musanta nasarar da ya samu a Legas ba,” in ji shi.

Da yake karin haske kan manufarsa zuwa Amurka, ministan ya ce, l ya je ne domin ya gyara munanan labaran da ‘yan ‘yan adawa ke yaɗawa kan zaɓen.

Ya ce, ‘yan adawa da suka sha kaye a zaɓen suna zargin an tafka maguɗi, suna masu ƙira da a soke zaben.

“Mun zo nan ne domin mu daidaita wannan gurbatattun labaran da kuma shaida wa duniya babu shakka cewa babban zaben da aka kammala a Nijeriya shi ne mafi gaskiya, kuma ingantacce a tarihin Nijeriya.

“Zaɓen shi ne mafi adalci kuma mafi inganci saboda ɓullo da tsarin tabbatar da masu kada ƙuri’a (BVAS) wanda na dauka a matsayin mai canza wasa.

Fasahar BVAS ta taimaka wajen kawar da aringizon kuri’u ga masu jefa ƙuri’a ba bisa ƙa’ida ba, hakan shi ne ya sa aka yi zaɓe sahihi ba tare da tashin hankali ba.

Dangane da rahoton na INEC, ministar ya ce, BVAS, a lokacin zaben, ta yi aiki kashi 97 cikin 100 ta ba da kwarin guiwa a zaɓen.

1 COMMENT

Leave a Reply