Gwamnatin tarayya ta bawa kamfanin jirgin sama na Tanzania lasisin fara jigila kai tsaye zuwa Legas 

0
132
Gwamnatin tarayya ta bawa kamfanin jirgin sama na Tanzania lasisin fara jigila kai tsaye zuwa Legas 

Gwamnatin tarayya ta bawa kamfanin jirgin sama na Tanzania lasisin fara jigila kai tsaye zuwa Legas

Daga Jameel Lawan Yakasai

Gwamnatin Tarayya ta bai wa kamfanin Air Tanzania lasisin gudanar da zirga-zirgar jiragen ƙetare domin fara tashi kai tsaye daga Dar es Salaam zuwa Lagos.

Babban Sakatare na Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama, Ibrahim Kana, ya ce matakin zai inganta tsaro, inganci da haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da Tanzania, tare da daidaita ayyukan jiragen sama da ƙa’idodin kasa da kasa.

KU KUMA KARANTA: Jirgin sama ya faɗo akan titin Sao Paulo ya kashe mutane 2

Hukumar NCAA ta bayyana cewa za a rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna wadda za ta wajabta wa ATCL ta saka bayanan fasinjoji a tsarin AVITECH kafin fara aiki.

Jakadan Tanzania a Najeriya, Selestine Gervas Kakele, ya gode wa Najeriya bisa wannan dama, yana mai cewa haɗin gwiwar zai magance matsalar rashin haɗin kai a zirga-zirgar jiragen sama a Afrika.

ATCL ta kammala shirin bin ka’idoji, kuma tana neman ofishi a Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da izinin zama ga ma’aikatanta.

Leave a Reply