Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun hutun ƙaramar Sallah

0
151

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Talata da Laraba mai zuwa a matsayin ranakun hutu domin gudanar da bukukuwan Sallah ƙarama.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya ranar Lahadi a Abuja.

Tunji-ojo, cikin saƙon taya murna da babbar sakatariyar ma’aikatar, Aishetu Gogo Ndayako ta fitar, ya taya al’ummar Musulmin Najeriya murnar kammala azumin watan Ramadan na wannan shekarar.

Ministan, ya buƙaci Musulmi da su yi koyi da kyawawan halaye, kyautatawa, soyayya, hakuri, zaman lafiya da kuma tausayi kamar yadda manzon Allah S.A.W, ya koyar.

KU KUMA KARANTA: Shirin gwamnatoci na ciyar da mabuƙata a watan Ramadan na cin karo da ƙalubalen zargin almundahana

Tunji-ojo, ya kuma buƙaci ’yan Najeriya da su ci gaba da kasancewa masu haɗin kai domin ɗorewar zaman lafiya a ƙasar nan.

A cewar sanarwar, “Ministan ya yi wa ɗaukacin al’ummar Musulmi barka da Sallah tare da addu’ar Allah ya ƙaro zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.”

Ana sa ran za a yi sallah a ranar Talata ko Labara da zarar an ga watan Shawwal na shekarar 1445 bayan hijira.

Leave a Reply