Gwamnatin Sakkwato ƙarƙashin Gwamna Ahmed Aliyu za ta fara tura ɗalibai zuwa ƙasashen waje domin su yi karatu.
Shugaban hukumar ba da tallafin karatu ta jihar, Abdulƙadir Ɗan’iya, ya ce a makon farko na watan Nuwamba ɗalibai 15 za su tafi China .
Ya ce za a ƙara ɗaukar nauyin ƙarin ɗalibai zuwa ƙasashen waje domin su karanta kwasa-kwasan da za su amfani al’umma.
Shugaban hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar Sakkwato, Abdulƙadir Ɗan’iya ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a ofishinsa ranar Juma’a.
Ya kuma yi bayanin cewa ɗaliban da za su ci gajiyar wannan tallafin karatu, za su karanci kwasa-kwasan injiniyarin daban-daban a ƙasar Sin.
Abudulƙadir Ɗan’iya ya kuma bayyana cewa za su bar ƙasar nan a makon farko ko kuma mako na biyu na watan Nuwamba mai zuwa a 2023 da muke ciki.
KU KUMA KARANTA: Gwamnan Yobe ya amince da ɗaukar ma’aikatan jinya 158, da ba da alawus ga ɗalibai 393
Shugaban hukumar ba da tallafin karatun ya ce: “A halin yanzu suna kan ɗaukar horo da kuma wayar da kai wanda ya zama wajibi saboda zaman da za su yi a ƙasar waje.”
“Tuni gwamnatin jihar Sakkwato ta biya masu kuɗin makaranta da sauran hidindimun da za su yi yayin zaman karatu a can ƙasar.”
Ya kuma shawarci ɗaliban da aka ɗauki nauyi a yanzu da su yi aiki tuƙuru kar su ba gwamnatin jihar Sakkwato kunya bisa yardar da ta ɗora a kansu.