Gwamnatin Najeriya za ta kashe Naira biliyan 13 don inganta wutar lantarki a Legas
Gwamnatin Najeriya ta amince da ware biliyoyin naira domin gyarawa da kuma inganta hanyoyin samar da lantarki a faɗin ƙasar, ciki har da naira biliyan 13 da za a kashe a jihohin Legas da Ogun.
BBC ta rawaito cewa Ministan Lantarki Adebayo Adelabu ya faɗa jim kaɗan bayan kammala zaman majalisar zartarwa ranar Laraba cewa sun amince da daftari huɗu domin inganta ɓangaren samar da lantarkin ƙasar.
Daftari na farko, in ji ministan, shi ne cigaba da biyan diyya ga mutanen da aka karɓi gine-gine ko kadarorinsu domin yin aikin isar da layukan lantarki ta wurin.
KU KUMA KARANTA: Kungiyar samar da wutar lantarki ta kasa tafa fara yajin aiki a Kano daga ranar yau Laraba
“Majalisa ta amince da biyan diyyar naira biliyan 13 a ƙarƙashin kamfanin lantarki na Lagos Transmission Industrial Project, wanda za a biya da bashin dala miliyan 238 da bankin Japan International Cooperation Agency (JICA) zai bayar,” a cewarsa.
“Sauran daftari ukun sun jiɓanci amincewa da shigo da na’urorin rarraba lantarki ne daban-daban domin maye gurbin waɗanda suka tsufa a babban layin lantarki na ƙasa.”









