Gwamnatin Najeriya ta yi ƙarin haske kan ziyarar da shugaba Tinubu zai kai Qatar

0
161

Fadar shugaban Najeriya ta yi zargin cewa wasu mutane “masu muguwar aniya” ne suka fitar da wata wasiƙa game da ziyarar da shugaban ƙasar Bola Tinubu zai kai Qatar a watan gobe.

Wasiƙar, wadda aka yi musaya tsakanin ofishin jakadancin Qatar da ke Abuja da ma’aikatar harkokin wajen Najeriya game da ziyarar kasuwanci da Shugaba Tinubu zai kai Qatar ranar 2 zuwa 3 ga watan Maris, ta jawo ce-ce-ku-ce ne bayan an yi zargin cewa gwamnatin Qatar ba ta so shugaban Najeriya ya je ƙasar.

Sai dai Bayo Onanuga, mai taimaka wa shugaban Najeriya kan watsa labarai da tsare-tsare, ya fitar da sanarwa da ke musanta cewa gwamnatin Qatar ba ta damu da ziyarar da Shugaba Tinubu zai kai ba.

KU KUMA KARANTA: Muna so shugaba Tinubu ya dawo da tallafin man fetur – Ƙungiyar ‘yan Arewa

“Muna masu sanar da cewa akwai dangantaka mai ƙarfi tsakanin ƙasashenmu biyu kuma muna so mu jaddada cewa Shugaba Bola Tinubu zai ziyarci Qatar ne bisa gayyatar da Sarkin Qatar, Mai Martaba Sheik Tamim Bin Hamad Al-Thani ya yi masa,” in ji Onanuga.

Kazalika wata sanarwa da Francisca Omayuli, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya ta fitar ranar Asabar ta tabbatar da cewa Shugaba Tinubu zai ziyarci Qatar domin “ƙarfafa dangantaka mai gwaɓi da ke tsakanin ƙasashen biyu.”

Ziyarar za ta mayar da hankali wajen bunƙasa harkokin kasuwanci da diflomasiyya da sauransu, a cewar gwamnatin Najeriya.

Leave a Reply