Gwamnatin Najeriya ta kafa kwamitin warware matsalar tashin farashin gas

Gwamnatin Najeriya ta kafa wani kwamiti na musamman don bibiyar yadda farashin iskar gas ta girki ke ci gaba da tashin gwauron zabi a sassan ƙasar.

Wata sanarwar ma’aikatar makamashi ta Najeriyar ta ruwaito minista Ekperikpe Ekpo na bayyana matuƙar damuwa da yadda farashin na gas ke ci gaba da tashi a sassan ƙasar.

A cewar ministan cikin ƙasa da mako guda kwamitin da aka ɗorawa alhakin warware matsalar zai shawo kan tsadar iskar ta gas da kuma aikin rarraba shi zuwa sassan Najeriya.

KU KUMA KARANTA: Amfani da iskar gas na dafa abinci a janareta yana taimakawa masu ƙananan kanfanoni

Rahotanni sun bayyana cewa, farashin gas ɗin na girki ya tashi daga naira 700 kan duk lita guda da ake saye a baya zuwa fiye da naira 900 a yanzu.

A wasu sassa na Najeriyar bayanai sun ce ana sayar da duk lita guda kan farashin fiye da naira dubu 1200.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *