Gwamnatin Najeriya ta fara tattaunawa da ‘yan kasuwa don karya farashin kayan abinci 

0
74
Gwamnatin Najeriya ta fara tattaunawa da ‘yan kasuwa don karya farashin kayan abinci 

Gwamnatin Najeriya ta fara tattaunawa da ‘yan kasuwa don karya farashin kayan abinci

A wani yunkuri na daƙile matsalar hauhawar farashi a Najeriya da kuma bayar da cikakkiyar kariya ga masu sayen kaya, Hukumar Kare Hakkin Masu Sayen Kaya (FCCPC), ta fara tattaunawa da masu ruwa da tsaki don warware matsalar.

Shugaban hukumar, Mista Tunji Bello a jawabin da ya gabatar gaban ƙungiyoyin ‘yan kasuwar da ke hada-hadar rarraba kaya a Najeriya, ya bayyana takaicinsa da yanayin yadda farashin kayan ke hauhawa ba tare da wani dalili ba, musamman kayayyakin da ake sarrafawa a cikin gida.

Matakin hukumar na zuwa a daidai lokacin da wani rahoton hukumar kididdiga ta Najeriya (NBS), ke cewa farashin kayayyaki musamman ɓangaren abinci ya yi matukar hauhawa a watan Yuni da kashi 34.2 cikin 100.

Hukumar ta ce wannan adadi ya ƙaru ne matuƙa daga hauhawar kashi 22.8 cikin 100 da al’umma suka gani a watan Yunin 2023.

KU KUMA KARANTA: Za mu raba wa jami’an tsaro tallafin abinci — Gwamnan Kano

Yanzu haka dai FCCPC na ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki daga ɓangarorin ‘yan kasuwa da masu hada-hadar rarraba kayaki a sassan Najeriya.

Idan ba a manta ba, hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa baya ga yunwa su ne, suka sanya ‘yan Najeriya fantsama titi inda suka yi zanga-zangar adawa da yanayin.

Sai dai zanga-zangar ta bar baya da kura a wasu yankuna, inda ta koma tashe-tashen hankula.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here