No menu items!

Sample Page Title

Date:

Daga Ibraheem El-Tafseer

Ministan harkokin cikin gida Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya a Abuja.

Tunji-Ojo ya taya al’ummar musulmin gida da na ƙasashen waje murnar zagayowar watan haihuwar Manzon Allah (S).

Ya kuma gargaɗi ‘yan Najeriya da su yi koyi da kyawawan halayen Manzon Allah (SAW), irin haƙuri, juriya da sauran kyawawan ɗabi’unSa.

Ministan ya kuma buƙaci ’yan Najeriya musamman matasa da su rungumi ɗabi’ar aiki tuƙuru da zaman lafiya da juna, ba tare da la’akari da bambamcin aƙida, da zamantake wa ba.

Ya kuma umarce su da su haɗa kai da gwamnatin shugaba Bola Tinubu a ƙoƙarinta na gina ƙasa mai ci gaba da kishi da ‘yan Najeriya za su yi alfahari da ita.

Tunji-Ojo ya yi wa al’ummar musulmi fatan alheri.(NAN)

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...