Gwamnatin Najeriya ta ƙara kuɗin fasfo 

0
179
Gwamnatin Najeriya ta ƙara kuɗin fasfo 

Gwamnatin Najeriya ta ƙara kuɗin fasfo

Hukumar shige da fice ta Najeriya (NIS) ta sanar da ƙarin farashin yin fasafo wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga Satumba, 2025, domin inganta inganci da tsaro a tsarin fasafo ɗin ƙasar.

A cewar hukumar, farashin fasafo na shekaru biyar mai shafi 32 wanda a baya yake kan naira 70,000 yanzu zai tashi zuwa naira 100,000, yayin da na shekaru 10 mai shafi 64 wanda a baya yake kan naira 120,000 zai koma naira 200,000.

KU KUMA KARANTA: Fasfo dubu 97 ba a karɓa ba a Najeriya – NIS

Sai dai, farashin fasafo da ‘yan Najeriya ke yi a ƙasashen waje ba zai canza ba, inda za a ci gaba da biyan dala 150 kan fasafo na shekara 5 da dala 230 kan fasafo na shekara 10.

Hukumar ta bayyana cewa wannan sabon tsarin na nufin tabbatar da daidaito a ayyukan fasafo, tare da sauƙaƙa damar samun fasafo ga duk ‘yan Najeriya.

Leave a Reply