Gwamnatin Najeriya ta ce ba ta da niyyar kafa sansanin sojojin ƙasashen waje a cikin ƙasar, kamar yadda Ministan Watsa Labarai Mohammed Idris ya faɗa a wata sanarwa.
“Gwamnatin tarayya na sane da ƙaryar da ake ta yaɗawa da ke cewa ana tattaunawa tsakanin gwamnatin tarayyar Najeriya da wasu ƙasashen ƙetare kan batun zaman sansanonin sojojin ƙasashen waje a ƙasar.
“Don haka muna ƙira ga jama’a da su yi watsi da wannan ƙaryar,” in ji sanarwar.
A kwanakin baya ne wasu rahotanni suka rinƙa yawo waɗanda ke nuna cewa Shugaban Najeriya Tinubu na shirin amincewa da ƙasashen Amurka da Faransa su mayar da manyan sansanoninsu Najeriya bayan ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso sun yi hannun riga da su.
KU KUMA KARANTA: EFCC ta kama tsohon Ministan Jiragen Sama, Hadi Sirika
Bayan hakan ne sai wasu daga cikin fitattu kuma masana daga arewacin Najeriya suka aika wasiƙa ga Shugaba Tinubu da Majalisar Tarayya, wadda aka rubuta ranar 3 ga watan Mayun 2024, suna buƙatar gwamnatin ta guji ɗaukar wannan matakin.
Amma sanarwar Minista Idris ta jaddada cewa babu wata tattaunawa da Gwamnatin Tarayya take yi da kowace ƙasar waje.
“Ba mu samu wata buƙata daga kowace ƙasa ba, kuma babu wani shiri da muke yi na na shirin kafa sansanon sojin kasashen waje a Najeriya ba.”
Gwamnatin Najeriyar ta ce tuni take samun haɗin kan kasashen waje wajen tunkarar ƙalubalen tsaro da ake fama da shi, kuma Shugaban Kasa ya ci gaba da jajircewa wajen zurfafa wannan ƙawance, da nufin cimma manufofin tsaron ƙasa na Ajandar Sabunta Fata.