Gwamnatin Kebbi ta ɗauki nauyin kai ɗalibai 70 karatu a Saudiyya
Daga Idris Umar,Zariya
Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen daukar nauyin dalibai 70 zuwa Masarautar Saudiyya domin karatun digiri a fannoni na addini da na zamani.
Wannan na daga cikin shirin “Kaura Capacity Building Project 2025“ karkashin ma’aikatar kula da harkokin addinai ta jihar.
A yayin wani taron manema labarai, mai bai wa Gwamna shawara kan harkokin addinali, Injiniya Imran bn Usman, ya bayyana cewa kowanne daga cikin kananan hukumomi 20 na jihar za su ba da sunayen dalibai uku, yayin da aka ware wa babban birnin jihar, Birnin Kebbi, guraben dalibai 10.
KU KUMA KARANTA:Cutar sanƙarau ta kashe mutane 55 a Kebbi
Ya bayyana cewa, gwamnatin jihar ce za ta dauki nauyin tafiyar daliban zuwa Saudiyya, yayin da gwamnatin Saudiyya za ta dauki nauyin karatunsu da walwalarsu bayan isarsu.
Mai ba da shawarar ya kara da cewa, ana sa ran kowacce karamar hukuma za ta gabatar da dalibai maza biyu da mace daya, don neman guraben karatun digiri a fannin addinin Musulunci ko sauran fannoni na zamani.
Ya kuma kara da cewa, an kammala shirin tura limaman masallatai Jumu’a zuwa kasashen waje domin horo na gajeren lokaci a fannin yadda ake gabatar da huduba da Hadisi, don kara inganta tasirinsu yayin gabatarda Sallah.