Gwamnatin Katsina ta rufe makarantun koyar da kiwon lafiya masu zaman kansu a jihar

0
47
Gwamnatin Katsina ta rufe makarantun koyar da kiwon lafiya masu zaman kansu a jihar

Gwamnatin Katsina ta rufe makarantun koyar da kiwon lafiya masu zaman kansu a jihar

Daga Idris Umar, Zariya

Gwamnatin Jihar Katsina ta ba da umarnin rufe dukkan cibiyoyin koyar da harkokin lafiya masu zaman kansu da ke aiki a jihar nan take tare da soke lasisoshinsu.

Wannan umarni ya fito ne daga bakin Umar Mammada Adamu, mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan cibiyoyin lafiya, bayan gano cewa akwai cibiyoyi masu zaman kansu da yawa da ba su yi rijista ba kuma sun saba ƙa’idodi da ke barazana ga lafiyar al’umma.

Da yake magana da ‘yan jarida, Mammada ya jaddada yawaitar irin waɗannan cibiyoyi da kuma haɗarin da suke haifarwa ga kiwon lafiyar jama’a.

“Da dama daga cikin waɗannan cibiyoyi ba su cika ƙa’idodin doka ba, kuma hakan yana kawo cikas ga ingancin horar da ma’aikatan lafiya a jihar,” in ji shi.

KU KUMA KARANTA: NAFDAC ta rufe wani kamfani a Legas mai samar da jabun kayan kwalliya

An yanke wannan shawara ne sakamakon bincike daga Ma’aikatar Lafiya ya nuna cewa akwai makarantu da yawa na koyar da harkokin lafiya masu zaman kansu da ba su da izinin gudanar da aiki, wanda ya jawo hankalin gwamnati.

Makarantun zasu ci gaba da zama a kulle har sai an sake yin cikakkiyar tantancewa tare da sabon tsarin yin rijista wanda aka shirya yi daga ranar 24 zuwa 25 ga Fabrairu, 2024.

An umarci masu cibiyoyin da abin ya shafa su gabatar da dukkan takardu masu muhimmanci ga kwamitoci na musamman don tabbatarwa.

“Wannan mataki ne mai muhimmanci don tsaftace tsarin kuma tabbatar da cewa duk cibiyoyin kiwon lafiya suna bin dokokin jihar,” in ji Adamu, yana mai tabbatar wa jama’a cewa gwamnati na da cikakken niyyar inganta matakan kiwon lafiya.

Leave a Reply