Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano za ta soma biyan albashi a tsarin IPPIS

Published

on

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da manhajar ɗaukar bayanan ma’aikatan gwamnati da ƴan fansho da ƴan siyasa wajen biyansu albashi a tsarin nan na IPPIS.

Tsarin IPPIS tsari ne da gwamnatin tarayyar Najeriya ta daɗe tana amfani da shi wajen biyan ma’aikatanta, inda ake ɗaukar bayansu ciki har da zanen yatsun hannu, da nufin rage rashin gaskiya da wasu ke yi na yin aiki a hukumomin gwamnati daban-daban suna karɓar albashi fiye da ɗaya.

A sanarwar da mai magana da yawun gwamnan Jihar Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ranar Talata, Gwamna Abba Gida-Gida kamar yadda aka fi saninsa, ya ce ya bijiro da wannan tsari ne don tabbatar da gaskiya da rashin rufa-rufa da ƙeƙe-da-ƙeƙe wajen tafiyar da al’amuran gwamnati.

Gwamnan ya ƙaddamar da tsarin da aka bai wa suna Kano Integrated Personal and Payroll Information System (KIPPIS) ne a wajen taron Majalisar Zartarwa karo na 12 da aka yi a fadar gwamnatin jihar.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta haramtawa gwamnatin Kano rusau a Jihar

Abba Gida-Gida wanda ya zamo mutum na farko da aka ɗauki bayanansa aka ɗora a kan manhajar tsarin, ya ce za a yi amfani da shi ne a duka matakin jiha da na ƙananan hukumomi “don bin tsarin sha’anin kuɗi da duniya ke kai a yanzu.”

Gwamnan ya nei mambobin kwamitin ƙaddamar da tsarin KIPPIS da su tabbatar da cewa sun ɗauki bayanan dukkan ma’aikatan gwamnati da ƴan fanshi da masu riƙe da muƙaman siyasa don samun nasarar tsari a faɗin jihar.

Kazalika Babban Akawun jihar Alhaji Abdulkadir Abdussalam, ya ce za a tabatar da cewa ba a samun matsaloli ba a wajen bin tsarin KIPPIS ta kowane fanni da suka haɗa da rage kuɗaɗen mutane.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Al'ajabi

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Published

on

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon bene mai hawa biyu a Jihar Legas, ya rushe yayin da ake tsaka da mamakon ruwan sama wanda ya haddasa ambaliya a wasu sassan jihar.

Ginin ya rushe ne a lamba 12 da ke yankin Cameroun kusa da Ewenla a Mushin.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (LASEMA), ta bayyana cewar bayan isar jami’anta wajen da lamarin ya faru, ta gano wani sabon gini mai hawa biyu ya rushe.

An ceto mutum bakwai; mata uku da maza huɗu, tuni aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

KU KUMA KARANTA: Wani bene mai hawa 4 ya rufta da mutane a Abuja

Ya zuwa yanzu dai hukumar, ta ce babu wanda ya mutu a dalilin rushewar ginin.

Babban sakataren LASEMA, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce ana ci gaba da gudanar aikin ceto don tabbatar da babu wanda ya maƙale a baraguzai.

Continue Reading

Labarai

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Published

on

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewar wani jami’in Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), ya hallaka kansa har lahira a Abuja.

An tsinci gawar marigayin ne a gidansa da ke babban birnin tarayya.

Marigayin, wanda ba a bayyana sunansa ba, an ce ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka yi kwas na 5 a makarantar horas da masu yi wa ƙasa hidima ta hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa.

An ruwaito cewar yana da ƙwazo da himma a wajen gudanar da ayyukansa.

Wata majiya ta ce jami’in ya jima yana fama da baƙin ciki da matsalolin rayuwa kafin mutuwarsa.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya shaida wa manema labarai cewa hukumar za ta binciki musababbin da ya sanya ya kashe kansa, kuma hukumar za ta taimaka wa iyalansa.

Oyewale, ya ƙara da cewa hukumar za ta binciki wasu abubuwa da suka haɗa da matsalar taɓin hankali da kuma matsalolin iyali waɗanda ka iya sanya ma’aikacin kashe kansa.

KU KUMA KARANTA: Ana zargin wani jami’in kwastam ya kashe kansa a Abuja

Sai dai ya ce hukumar ba za ta fitar da wata sanarwa ko kuma bayyana sunan jami’in ba, har sai an kammala bincike.

Continue Reading

Labarai

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Published

on

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta rufe shaguna kusan 100 a babbar kasuwar Ogbete ta Jihar Enugu, bisa zargin sayar da wasu abubuwan sha na jabu.

Daraktan NAFDAC, Martins Iluyomade a yankin Kudu maso Gabas, ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne bayan wani samame da ta kai a ranar Litinin.

A yayin samamen jami’an hukumar NAFDAC, sun cafke wata babbar mota ɗauke da kayayyakin maye tare da cafke wasu ‘yan kasuwa huɗu da ake zargi da hannu wajen sayar da jabun abubuwan sha.

Iluyomade, wanda masanin haɗa magunguna ne, ya nanata cewa matakin ya zama dole domin kare masu amfani da ire-iren kayayyakin .

Ya ce waɗanda ake zargin a halin yanzu ana kan bincikensu kuma za su fuskanci tuhuma a gaban kotu bayan kammala binciken.

KU KUMA KARANTA: NAFDAC ta haramta amfani da maganin tari na yara na kamfanin J&J

Har wa yau, ya nanata ƙudurin NAFDAC na kawar da kayayyaki marasa inganci, da jabun abubuwan ci da sha, da gurɓatattun kayayyaki a kasuwa.

Ya ƙara da cewa, an gudanar da binciken ne tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro.

A gefe guda kuma, ya bayyana muhimmancin aikin hukumar na tabbatar da lafiyar al’umma.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like