Gwamnatin Kano za ta kafa rundunar tsaro a makarantu a Hedkwatar NSCDC

0
30
Gwamnatin Kano za ta kafa rundunar tsaro a makarantu a Hedkwatar NSCDC

Gwamnatin Kano za ta kafa rundunar tsaro a makarantu a Hedkwatar NSCDC

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta shirya kafa Cibiyar Tsaron Makarantu a Hedkwatar Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) a Kano.

Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Alhaji Umar Haruna Doguwa, a lokacin taron wayar da kan jama’a na yini ɗaya kan aiwatar da shirin Tsaron Makarantu.

Taron mai taken “Fahimtar Asalin Tsaron Makarantu” an yi shi ne don ƙara fahimtar mahimmancin tsaro a makarantu.

A wata sanarwa da Ibrahim Idris Abdullahi, jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar Tsaron Fararen Hula reshen Kano ya fitar a ranar Laraba, Haruna Doguwa ya yabawa sadaukarwar NSCDC wajen tabbatar da tsaron cibiyoyin ilimi a fadin jihar.

Ya jaddada cewa wannan tsari zai samar da tsaro mai muhimmanci ga makarantu, wanda zai baiwa malamai da dalibai damar koyarwa da koyo a yanayi mai aminci.

Kwamishinan ya kuma yi godiya ga haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro na jihar, wanda ya ce shi ne ya taimaka wajen ci gaba da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kano.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga satar makaman jami’an tsaro suka yi – Ministan Tsaro

A madadin Gwamna Yusuf, Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Ayyuka na Musamman na Jihar Kano, Manjo Janar M. I. Idris (mai ritaya) ya yabawa rawar da NSCDC ke takawa wajen kare makarantu a jihar.

Ya sake tabbatar da aniyar gwamnatin na kara inganta matakan tsaro, musamman a makarantu, wadanda suka fara zama wani matattarar hare-haren yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

A jawabinsa na bude taron, kwamandan NSCDC na Jihar Kano, Mohammed Lawal Falala, ya yi bayanin muhimmancin shirin Tsaron Makarantu. Ya jaddada cewa wannan shiri yana da matukar muhimmanci wajen magance barazanar tsaro da makarantu ke fuskanta daga yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka.

Kwamanda Falala ya kuma godewa Gwamnatin Jihar Kano bisa goyon bayan da take ci gaba da bayarwa

Leave a Reply