No menu items!

Sample Page Title

Date:

Gwamnatin Kano za ta gina gidaje kyauta ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa

Gwamnatin jihar Kano ta yi alƙawarin gina gidaje kyauta ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a faɗin ƙananan hukumomi 44 na jihar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamna jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce za a yi hakan ne don rage raɗaɗin da ambaliyar ta haifar a jihar.

Dawakin Tofa ya ce, Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan a yayin zaman majalisar zartarwa da ya gudana a fadar gwamnatin Kano a jiya Laraba.

Ya ambato Gwamnan na bayanin cewa gidajen da za a samar za taimakawa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa wajen samun matsuguni ga iyalansu.

KU KUMA KARANTA:Gwamnan Kano ya rushe shugabannin ƙananan hukumomin jihar 44

Ya ce, gwamnatin jihar na haɗa gwiwa da ma’aikatar jinƙai da yaƙi da talauci domin taimakawa mutanen da kayan abinci da abubuwan rayuwa na yau da kullum.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar na shirin raba kujeru da ababen zama a mataki na farko ga daliban makarantun firamare da Sakandare 220, 000 domin inganta fannin koyo da koyarwa.

Gwamna Yusuf, ya ce bisa ayyana dokar tabaci a fannin ilimi a jihar, gwamnatin zata raba kayan makaranta na sawa ga dukkan daliban ajin farko na makarantun firamare.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...