Gwamnatin Kano za ta gina gadar sama da ta ƙasa, a wasu muhimman wurare a jihar

0
222

Gwamnan jahar Kano ya aikewa da majalisar jahar Kano ɗan ƙwarya-ƙwaryar kasafin kuɗi kimanin sama da naira biliyan 58.

Rahotanni sun ce kasafin Kuɗin ya ƙunshi gina gadar Sama da ta ƙasa a sha-tale -talen Titin Ƙofar Ɗan’agundi da Tal’udu, don rage cunkosan ababen hawa, anyi la’akari da tituna ne da ke da alaƙa da yawancin manyan makarantun gaba da sakandire a jahar Kano.

Haka kuma kasafin yana ƙunshe da harkar ilimi, wanda ke da kaso mafi tsoka a cikinsa, gyaran makarantun sakandire da ɗaukar nauyin ‘ya’yan jahar Kano zuwa karatu ƙasashen waje, wato digiri na biyu (Msc).

A harkar lafiya kuma, abubuwan da suka haɗa da gyare-gyaren Asibitoci dama sanya na’urorin aiki na zamani, haihuwa kyauta da ba da magani kyauta,, da sauran buƙatu na ɓangaren lafiya.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta umarci gwamnatin Kano ta biya diyyar rushe-rushen shagunan ‘yan kasuwa a jihar

Ɓangaren Auren Zawarawa! Don ragewa Al’umma raɗaɗi da cika musu burukan su na aiwatar da sunnar Annabinmu tsira (S.A.W). Da sauran manyan Ayyukan rayar da Al’umma.

Shugaban kwamitin tsare-tsare na majalisar jahar Kano ne ya bayyana hakan bayan zaman majalisar na ranar juma’a.

Leave a Reply