Gwamnatin Kano za ta ci tarar dubu 25 ga duk wanda ya tofar da yawu a faɗin titunan Kano

0
22
Gwamnatin Kano za ta ci tarar dubu 25 ga duk wanda ya tofar da yawu a faɗin titunan Kano

Gwamnatin Kano za ta ci tarar dubu 25 ga duk wanda ya tofar da yawu a faɗin titunan Kano

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta kafa dokar da zata tilastawa duk wanda aka kama yana tofar da yawu, yin fitsari, bayan gida, ko zubar da shara akan tituna, da karkashin gadoji, inda ta sanya kudi kimanin Naira Dubu Ashirin Da Biyar 25,000 amatsayin tara ga wanda aka kama da aikata daya ciki.

Wannan doka na zuwa ne bayan Majalisar ta amince da kudurin doka da zai bai wa hukumar da ke da alhakin kyautata kyawun birnin Kano da kula da wuraren shakatawa damar aiwatar da aikinta yadda ya kamata.

KU KUMA KARANTA:An harbe mutane 4 a rikicin da ya ɓarke tsakanin jama’a da jami’an tsaro kan rusau a Kano

Da yake zantawa da manema labarai bayan zaman Majalisa na ranar Litinin, Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Lawan Hussaini Dala, ya bayyana cewa dole ne gwamnati ta dauki matakan tsaftace Kano domin saka jihar a sahun manyan biranen duniya wajen tsafta da cigaba.

Lawan Hussaini Dala ya kara da cewa, baya ga tarar naira dubu ashirin da biyar, akwai wasu hukunci da doka ta tanada domin ladabtar da duk wanda aka samu da aikata wadannan laifuka.

Leave a Reply