Gwamnatin Kano za ta ɗauki masu gadin makarantu guda 17,600

0
57
Gwamnatin Kano za ta ɗauki masu gadin makarantu guda 17,600

Gwamnatin Kano za ta ɗauki masu gadin makarantu guda 17,600

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta kammala shirye-shiryen ɗaukar ma’aikata 17,600 na masu tsaron makarantu da kuma mafarauta na gida domin tabbatar da tsaro ga makarantun gwamnati a ƙananan hukumomi 44 na faɗin jihar.

Kwamishinan Ilimi, Alhaji Umar Doguwa ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a Kano lokacin da ya karbi bakuncin mambobin zartarwa na kungiyar tsofaffin daliban makarantar Rumfa, ajin ’94, waɗanda suka ziyarce shi.

A cewarsa, samar da tsaro zai taimaka matuka wajen kare yara daga barazanar iri-iri. Doguwa ya bayyana cewa, domin ilimi ya ci gaba, akwai bukatar hadin gwiwa tsakanin gwamnati, jama’a da kungiyoyin da ba na gwamnati ba domin magance matsalolin da ke tattare da bangaren ilimi.

KU KUMA KARANTA:Gwamnan Kano ya ba da tallafin Naira Miliyan 100 ga waɗanda gobara ta shafa a kasuwar Kantin Kwari.

Kwamishinan wanda ya samu wakilcin babbar sakatariyar ta ma’aikatar, Hajiya Kubra Imam, ta tabbatar da shirye-shiryen ma’aikatar na aiki tare da kungiyoyin tsofaffin dalibai a fadin jihar domin inganta darajar ilimi.

Kwamishinan ya ce, aniyar gwamnatin kwanan nan na ayyana dokar ta baci a bangaren ilimi wata shaida ce ta gwamnan jihar, Abba Kabir-Yusuf, na neman magance matsalolin ilimi.

Leave a Reply