Gwamnatin Kano tana yunƙurin ƙwace mana gonaki – Al’ummar Fanisau

0
22
Gwamnatin Kano tana yunƙurin ƙwace mana gonaki - Al'ummar Fanisau

Gwamnatin Kano tana yunƙurin ƙwace mana gonaki – Al’ummar Fanisau

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Al’ummar Fanisau dake yankin ƙaramar hukumar Ungogo a Jihar Kano, sun zargi gwamnatin Kano da yunƙurin ƙwace musu gonakinsu, waɗanda suka gada daga iyaye da kakanni.

KU KUMA KARANTA:Wasu ɓarayi sun girbe gonakin shinkafa a Taraba

Mazauna yankin sunce sun wayi gari da ganin allo na kwamitin kar ta kwana kan filaye da gine gine na gwamnatin Kano Knupda,

Inda suka bukaci gwamnan Kano Alh. Abba Kabir Yusuf ya taimaka ya kawo musu dauki, kar a maimaita irin abun da ya faru a Rimin Zakara.

Leave a Reply